Wurin Tarihin Sadarwa
Tun kimanin shekaru dubu 3 da syuka gabata Iran tana da tsarin da take yin amfani da shi na aikewa da sakonni a lokacin sarakunan Hakhamanshiyawa. A lokacin Iran ta kasance babbar daula ce wadda ta hada yankuna da dama a cikin Asia da kuma gabas ta tsakiya, saboda haka tana da tsarin tafiyar da ayyukanta, daga ciki hard a tsarin aikewa da sakonni wanda zai isa ga dukkanin bangarorin da suke a karkashin wannan daula ta lokacin. Baya ga haka kuma ana kallon wannan tsarin aikewa da sakon shi ne irinsa na farko a tarihin dauloli. Ranar 9 ga watan Oktoba dai ita ce ranar aikewa da sako ta duniya.