Mohammed Amin Mujib, fitaccen makarancin kasar, ya karanta aya ta 139 na cikin suratul Al-Imran mai albarka domin shiga cikin yakin neman nasara bayan hare-haren da gwamnatin sahyoniya ta kai wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran da kamfanin dillancin labaran IQNA ke shiryawa.
Imam Sadik (AS) ya tambayi daya daga cikin sahabbansa cewa: Sau nawa ka yi aikin Hajji? Sai ya ce: Hajji goma sha tara. Sai Imam ya ce: Ka kara zuwa Hajji ka cika ashirin domin a rubuta maka ladan ziyarar Hussaini (AS) sau daya. [Kamil al-Ziyarat, shafi na 162].
IQNA - A cikin duniyar hayaniya da gaggawa ta yau, wani lokaci muna buƙatar ɗan ɗan dakata mai ɗan gajeren hutu. Tarin "Muryar Wahayi" tare da zaɓin mafi kyawun ayoyin Alqur'ani, gayyata ce zuwa tafiya ta ruhaniya da ban sha'awa.
IQNA – Hotunan da aka dauka a karshen watan Yulin shekarar 2025, sun nuna sakamakon harin ta’addancin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kai kan birnin Tehran na kasar Iran a cikin watan Yuni, wanda ya auka wa wuraren zama.