IQNA

Mai binciken daga Ingila ta ce:

Ziyarar Arbaeen; Gabatarwa don kammala canji a duniya

19:19 - September 08, 2023
Lambar Labari: 3489780
Karbala (IQNA) Wata mai bincike a kasar Ingila ta yi imanin cewa, idan har masoya Imam Hussain (AS) a duk fadin duniya suka hada hannu suka zama wani karfi na gaske wajen sauya yanayin tsarin duniya; Tattakin Arbaeen na shekara-shekara na iya zama share fage ga cikakken sauyi a duniya.

Tattakin Arba'in da aka gudanar da shi a 'yan shekarun nan, yana a matsayin wani lamari na siyasa na zamantakewa, ya ja hankalin masu tunani da bincike na duniya.

Mai bincike daga Ingila ta ce idan har masoya Imam Hussaini (AS) a duk fadin duniya suka hada karfi da karfe za su iya kawo sauyi a tsarin duniya.

A wata hira da ta yi da kamfanin dilalncin labaran Iqna, Rebecca Masterton ta amsa tambayar cewa a kowace shekara miliyoyin mutane daga sassa daban-daban na duniya suna tafiya ta tsawon kilomita goma a tarukan Arbaeen, menene ra'ayin ku game da wannan tattaki? ta ce: Tafiya daga Najaf zuwa Karbala, tun bayan kifar da Saddam Husaini, ya zama alama ce ta ibada ga Allah da Annabi Muhammad (SAW) da alayensa.

Kafafen yada labarai da masu fada a ji da masu yawon bude ido na kasashen yamma suna kara fahimtar wannan al'ada sannu a hankali.

Ta amsa tambayar cewa tattakin Arbaeen shi ne taro mafi girma na shekara-shekara na mutane a duniya, wanda a zahiri alama ce ta nuna adawa da duk wani nau'i da bayyanar ta'addanci, mulkin mallaka, zalunci.

 

4166712

 

Abubuwan Da Ya Shafa: karbala arbaeen hankali mulkin mallaka masoya
captcha