IQNA

Fair Observer : Ziyarar Arbaeen ta cancanci a rubuta ta a cikin littafin Guinness

15:37 - September 03, 2023
Lambar Labari: 3489750
Washington (IQNA) Shafin yada labarai na Fair Observer ya rubuta cewa: Kasantuwar miliyoyin mazoyarta daga kasashe da dama da addinai da imani daban-daban a taron tattakin na Arbaeen ya sanya masana ilimin zamantakewa da na addini da dama ke sha'awar wannan lamari. A cewar wasu masu lura da al'amura, wannan taron ya kasance na musamman ta hanyoyi da yawa kuma ya cancanci a rubuta shi a cikin littafin Guinness.

kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, gagarumin tattakin Arba’in yana jan hankalin masu kallo a duk shekara.

 Kasancewar miliyoyin masu ziyara daga kasashe da dama na duniya da mabanbantan addinai da imani a wani lamari na musamman ya sanya masana ilimin zamantakewa da na addini da dama sha'awar wannan lamari.

Shafin yanar gizon Fair Observer ne na Amurka wanda ya bayyana kansa a matsayin "mai zaman kansa" da "marasa riba" a cikin sashin gabatarwa. Wannan ma’adanar bayanai na wallafa abubuwan da mutane 2,500 daga kasashe 90 daban-daban suka gabatar bayan tantancewa sannan kuma tana da bangaren ilimi da ke ba da horo ga masu sauraro da masu sha’awar hanyoyin sadarwa na zamani, da rubuce-rubuce da dai sauransu.

Wani bincike kan tattakin Arbaeen da Mahdi Alavi, ya yi, mai fafutukar kare hakkin bil adama a Amurka, ya rubuta takaitaccen bayani wanda zaku iya karantawa a kasa: Ana ci gaba da shirye-shiryen babban aikin ziyara na shekara-shekara a duniya.

Miliyoyin jama'a ne suka hallara a birnin Karbala na kasar Iraki domin halartar taron Arbaeen, taron da ya kawo karshen zaman makokin 'yan Shi'a na kwanaki arba'in na shahadar Imam Hussain. A ko wace shekara ‘yan Shi’a tare da mabiya sauran addinai na gudanar da tarukan tunawa da Husaini jikan  Manzon Allah da ya yi shahada a Karbala.

Ya kamata a rubuta Arbaeen a cikin littafin Guinness Book of Records a wurare da yawa: taro mafi girma na shekara-shekara, tebur mafi tsayi, mafi yawan adadin mutane da ake ciyar da su kyauta, mafi yawan rukunin masu aikin sa kai da ke aiki a wani taron, duk da an bayyana su.

 

4166474

 

captcha