Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, tun a ranar Asabar din da ta gabata ne aka fara aiwatar da shirin na musamman na gwamnatin Iraki na samar da hidima ga alhazai daga ciki da wajen kasar.
Tahsin al-Khafaji, kakakin rundunar hadin gwiwa ta Iraki ya sanar a jiya Juma'a cewa, an samar da cikakken hangen nesa kan shirin na musamman na Arbaeen na bana.
Masu ziyara daga kasashen waje sun haura mutane miliyan 5 Yayin da yake hasashen halartar mahajjata daga kasashen waje sama da miliyan biyar a kasar Iraki domin gudanar da bukukuwan Arba'in, ya ce: A bana adadin Masu ziyara zai zarce na shekarun baya.
Al-Khafaji ya jaddada cewa: A baya-bayan nan jami'an tsaro sun gudanar da ayyukan leken asiri da kuma samame na musamman kan ragowar kungiyar ta'addanci ta Da'ish a wasu larduna da dama.
Babban kwamandan tsaron kasar Irakin yayin da yake jaddada cewa 'yan kungiyar ta Da'ish sun sha fama da munanan raunuka daga jami'an tsaro a baya-bayan nan, ya ce: Kungiyoyin tsaron Irakin domin karfafa tsaro a manyan hanyoyin tattakin Arba'in da kuma hanyoyin motocin masu ziyara don tsara zirga-zirgar dukkan iyakoki.