IQNA

An sake kona kur'ani mai girma a gaban ofisoshin jakadancin Turkiyya da Iraki a Denmark

19:40 - August 13, 2023
Lambar Labari: 3489634
Copenhagen (IQNA) Wasu masu wariyar launin fata da kyamar Musulunci a kasar Denmark sun kona kur'ani mai tsarki a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da Iraki.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiya 12 ga watan Agusta, mambobin wata kungiya mai suna ‘yan kishin kasar Denmark, sun kona kur’ani mai tsarki a gaban ofishin jakadancin Turkiyya da ke birnin Copenhagen.

Mambobin wannan kungiya sun kuma cinna wa wani kur'ani wuta a gaban ofishin jakadancin Iraki da ke Denmark.

Wadanda suka halarci wadannan ayyuka sun rike alluna da kuma rera taken nuna adawa da Musulunci tare da buga wadannan fage a cikin sararin samaniya ta hanyar watsa shirye-shirye kai tsaye.

An gudanar da wadannan ayyukan tada hankali ne a karkashin inuwar 'yan sandan kasar Denmark.

Zagin kur'ani mai tsarki a kasashen Sweden da Denmark na kara ta'azzara a 'yan kwanakin nan, kuma kungiyar 'yan kishin kasa ta kasar Denmark na ci gaba da maimaita yanayin wariyar launin fata a kullum a gaban ofisoshin jakadanci da masallatai na kasar tare da goyon bayan 'yan sandan kasar.

Wadannan kona kur'ani sun kasance tare da martanin da yawa daga kasashen Larabawa da na Musulunci; Hakan dai na faruwa ne duk da cewa kasar Denmark ba ta mai da hankali kan wadannan martanin ba, sannan kuma ba ta daukar wani mataki na musamman na tausaya wa musulmi da kuma hana maimaicin kona kur'ani.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4162081

captcha