IQNA

Makamiai masu linzami na ‘yan gwagwarmaya sun nufi Tel Aviv da matsugunan yahudawan sahyoniya

17:17 - May 11, 2023
Lambar Labari: 3489125
Tehran (IQNA) A ci gaba da mayar da martani kan sabbin hare-haren da gwamnatin sahyoniyawa ta kai a zirin Gaza, gwagwarmayar Palasdinawa ta kai hari kan Tel Aviv da ma matsugunan yahudawan sahyoniyawan Gaza da makaman roka.

A rahoton Falasdinu Ilyum, a yau tsakar rana ne gwamnatin yahudawan sahyoniya ta fara kai sabbin hare-hare kan yankuna daban-daban na zirin Gaza.

A cewar majiyoyin kiwon lafiya akalla mutum guda ne ya mutu sakamakon harin da mayakan gwamnatin sahyoniyawan suka kai a gabashin Khan Yunis, inda suka auna wasu gungun manoma a gonakinsu.

A halin da ake ciki dai gwamnatin yahudawan sahyoniya ta kai hari a yankunan Al-Qararah da Absan al-Kabirah da ke gabashin Rafah da kuma arewacin zirin Gaza, inda aka yi shahada daya da jikkata wasu da dama, kuma akalla yara biyu na daga cikin wadanda suka jikkata.

 

4140063

 

 

captcha