Babban masallacin Sultan Qaboos Da yake a birnin Muscat shi ne masallaci mafi girma a kasar Oman, domin yana daukar masu ibada kusan 25,000, da kuma gine-gine masu ɗaukar ido, masallacin na ɗaya daga cikin wuraren yawon buɗe ido a cikin ƙasar wadda ke yankin Tekun Fasha.