IQNA

Dan wasan takobi na Kuwait ya ki fuskantar abokin karawarsa bayahuden sahyoniya

16:59 - April 05, 2022
Lambar Labari: 3487129
Tehran (IQNA) Masu fafutuka a shafukan sada zumunta na Larabawa sun yaba wa 'yan wasan takobi na kasar Kuwait da ya ki fuskantar dan wasan sahyoniya a gasar wasan takobi ta Dubai.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-jazeera cewa, masu fafutuka na kasashen Larabawa sun yabawa dan wasan tawagar kasar Kuwaiti, Mohammad Al-Fadhli da ya ki fuskantar dan wasan yahudawan sahyoniya a gasar duniya a Dubai.

Wannan dai ba shi ne karon farko da wannan dan wasan dan kasar Kuwait din yaki yin wasa da bayahuden Isra'ila ba, a baya dai ya janye daga gasar wasan  ta duniya na shekarar 2019 a kasar Netherlands saboda kin karawa da  wani dan wasan sahyoniyawan, wanda masu adawa da salon daidaitawa da gwamnatin mamaya suka yi maraba da shi.

Majagaba a shafukan sada zumunta sun yaba da matakin al-Fadhli wanda ya yi daidai da tsayin daka da Kuwait ta dauka na goyon bayan al'ummar Palastinu.

A cikin 'yan watannin da suka gabata, wasu 'yan wasa daga bangarori daban-daban na kasar Kuwait, sun ki fuskantar abokan hamayyarsu yahudawan sahyuniya domin nuna goyon baya ga al'ummar Palastinu.

 

 

 

https://iqna.ir/fa/news/4046849

captcha