Jaridar Bawabul Ahram ta bayar da rahoton cewa, a jiya musulmin kasar Jamus sun gudanar da bikin da suke kira ranar bude kofin masallatai a fadin kasar.
An kwashe tsawon shekaru kusan 25 ana gudanar da wannan biki, inda akan bude masallatai tare da gayyatar sauran mabiya addinai da su ziyarci masallatai domin ganin yadda musulmi suke gudanar da ahrokinsu an addini.
Baya ga haka kuma ana bayar da dama ga dukkanin masu bukatar yin tambaya kan wani abu da ya shige musu duhu dangane da addinin muslunci, domin kara musu bayani.
A jiya ne dai 3 ga watan Oktoba ake gudanar da bukukuwan tunawa da ranar hadewar kasar Jamus ta yamma da gabas, inda musulmin kasar suka sanya wannan ranar ta zama ranar bude kofofin masallatai.