IQNA

Isra’ila Na Shirin Korar Dubban Falastinawa Daga Unguwanninsu A Birnin Quds

23:20 - May 26, 2021
Lambar Labari: 3485952
Tehran (IQNA) Isra’ila na Shirin korar wasu dubban wasu Falastinawa daga unguwanninsu a cikin birnin Quds.

Magajin garin birnin Kudus, Adnan Gaith ya bayyana cewa; Birnin na Kudus yana fuskantar takurawa mai tsanani da bai taba ganin irin ta ba a baya, da ta hada da killace mazaunansa da korarsu.

Har ila yau Adnan Gaith ya ce; HKI ta saki linzamin yahudawa ‘yan share wuri zauna suna kai wa birnin hari da kuma barnata wurarensa na tarihi,lamarin da yake damun mazauna wannan birni.

Bugu da kari, magajin garin birnin na Kudus ya ce; Kusan kwanaki hudu a jere kenan da ‘yan sahayoniya suke kama mazauna birnin da yin kutse cikin gidajen mutane suna dauke da manyan makamai saboda su firgita mutane.

Kafafen watsa labarun harshen Hebrew sun bayyana cewa; A karkashin dokar tattabar da tsari, za a kame duk wanda ya shiga cikin zanga-zangar da aka yi a cikin watan azumi ta nuna kin yarda da kwacewa Palasdinawan gidajensu, wacce ta kai ga yin yaki tsakanin ‘yan gwagwarmaya da Isra’ila.

Sai dai magajin garin na Kudus ya kara da cewa; Da akwai kwararrun lauyoyi, da suke bin diddigin abinda yake faruwa da kuma ziyartar wadanda aka kama saboda taimaka musu.

Dangane da Masallacin Kudus kuwa, magajin garin na birnin Kudus ya ce; Har yanzu yahudawa ba su daina yin kutse a cikin masallacin ba.

 

3973982

 

 

captcha