IQNA

Wurin Adana Kayan Tarihin Musulunci A Kasar Australia

22:26 - February 09, 2021
Lambar Labari: 3485634
Tehran (IQNA) wurin adana kayan tarihin muslunci na kasar Australia a gundumar Melbuorne.

A bisa rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, an bayyana wurin adana kayan tarihi na yankin Turnbury da ke cikin gundumar Melbourne da cewa, yana daga cikin muhimman wurare masu daukar hankula a kasar.

An gina wannan wuri ne tun a cikin shekara ta 2010 kuma an kashe tsabar kudi da suka kai dala miliyan 10, inda gwamnatin kasar Australia ta dauki nauyin bayar da kashi 20 cikin dari na dukkanin kudaden da aka kashe domin gina wurin.

An bude wurin ne a hukumance a cikin shekara ta 2014, wanda kuma a halin yanzu wurin yana karbar mutane har da masu yawon bude ido.

An saka kayayyaki masu nuna abubuwa daban-daban da suka shafi addinin muslunci, wadanda ke bayyana tarihi da kuam wasu muhimman lamurra da suke da dangantaka da muslunci.

Wani daya daga cikin musulmin kasar ta Australia ne ya yi tunanin gina wannan wuri a matsayin wata hanya ta nuna wa mutane abubuwa da suka shafi muslunci.

 
موزه اسلامی استرالیا و ساختمان خاص و منحصر به فرد آن + ویدئو
 
موزه اسلامی استرالیا و ساختمان خاص و منحصر به فرد آن + ویدئو
 
موزه اسلامی استرالیا و ساختمان خاص و منحصر به فرد آن + ویدئو
 
موزه اسلامی استرالیا و ساختمان خاص و منحصر به فرد آن + ویدئو

3952574

 

 

 

 

 

captcha