IQNA

Babban Malamin Quds Ya Yi Allawadai da Keta Alfarmar Masallacin Aqsa Da Yahudawa Suke Yi

22:44 - December 17, 2020
Lambar Labari: 3485468
Tehran (IQNA) Babban malami mai bayar da fatawa a birnin Quds ya yi Allawadai da kakkausar murya kan keta alfarmar masallacin aqsa mai alfarma da yahudawa suke yi.

Shafin yada labarai na Al-sharq ya bayar da rahoton cewa, Sheikh Muhammad Hussain Babban malami mai bayar da fatawa a birnin Quds ya yi Allawadai da kakkausar murya kan keta alfarmar masallacin aqsa mai alfarma da yahudawa suke yi da sunan raya wasu ranakun idinsu.

Ya ce abin da yahudawan sahyuniya suke yin a kutsa kai a cikin masallacin Quds mai alfarma a kowane lokaci suka ga dama, yana a matsayin tsokana ne ga musulmi, domin kuwa masallacin quds a matsayin alkiblar musulmi ta farko, wuri ne mai alfarma a cikin addinin muslunci.

Haka nan kuma ya yi ishara da yadda gwamnatin yahudawan Isra’ila take mara baya ga masu aikata hakan, inda takan bayar da daruruwan jami’an tsaro domin su ba su kariya, a lokacin da suke keta alfarmar wannan masallaci mai alfarma.

Wannan dai an zuwa a daidai lokacin da kasashen musulmi da na larabawa suke nuna halin ko in kula da abin da yahudawan suke yi a a kan masallacin quds, kuma babu wani katabus da suke yi domin takawa Isra’ila burki, sai ma kokarin kulla alaka da ita da wasu suke yi.

3941636

 

 

captcha