IQNA

Koriya Ta Kudu Na Kokarin Jawo Musulmi Domin Zuwa Bude Ido A Kasar

22:41 - September 08, 2020
Lambar Labari: 3485163
Tehran (IQNA) kasar Koriya ta kudu tana kokarin ganin ta jawo hankulan musulmi domin zuwa bude ido a kasar.

Shafin yada labarai na Asi One ya bayar da rahoton cewa, hukumar kula da harkokin yawun bude a kasar Koriya ta kudu, ta kirkiro da wani shiri na jawo hankulan musulmi domin ziyartar kasar.

A kan haka wannan hukuma ta bude wata wata talabijin mai zaman kanta mai suna Halal TV, domin nuna wurare masu ban sha'awa  a kasar, da kuma wurare wadanda musulmi za su iya samun abincin halal da suke bukata.

Tun kafin wanann lokacin dai hukumar kula da yawon bude ta kasar Koriya ta kudu ta jima tana nazarin hanyoyin da za ta kara bunkasa shigowar musulmi a cikin kasar, sakamakon yadda musulmi suka rage zuwa kasar a baya-bayan nan, saboda matsalar rashin abubuwan da suke da bukatuwa gare su, musamman abincin halal.

Musulmin kasashen Asia ne dai suke gudanar da ayyukan samar da abincin halal a cikin kasar Koriya ta kudu.

3921594

 

captcha