IQNA

Kalaman Sudais Kan kulla Alaka Da Yahudawan Isra’ila Sun Bar Baya Da Kura

22:58 - September 06, 2020
Lambar Labari: 3485157
Tehran (IQNA) Kalaman da limamin masallacin Haramin makka mai alfarma Abdulrahman Sudais ya yi na neman halasta kulla alaka da yahudawan Isra’ila, sun bar baya da kura.

A cikin hudubarsa ta Juma’a a wannan makoa  masallacin haramin Makka mai alfarma a dakin ka’abah, Abdulrahman Sudais ya bayyana cewa, bai kamata musulmi su rika nuna kin kulla alaka da wadada ba musulmi ba.

Ya ce saboda ta haka ne za a jawo wadanda ba musulmi ba zuwa ga addinin muslunci, domin kuwa manzon Allah SA) ya zauna da yahudawa a Madina kuma bai taba munana mu’amala da su ba, da nufin jawo su zuwa ga addinin muslunci.

Abdulrahman Sudais wadanda daya ne daga cikin fitattun malaman gwamnatin Saudiyya, baya kallon kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila da hadaddiyar daular larabawa ta yi a matsayin laifi, domin kuwa gwamnatin Saudiyya bata kallon hakan a matsayin laifi.

Da dama daga cikin larabawa masu bin shafukan zumunta na yanar gizo sun taso malamin a gaba, tare da bayyana matsayar tasa  a matsayin cin amanar addini, domin kuwa gwamnatin Isra’ila tana wakiltar yahudawan sahyuniya masu tsanain kiyayya da musulmi wadanda suka kwace kasar musulmi ta falastinu.

Yahudawan sahyuniya sun kashe dubban falastinawa sun kori miliyoyi daga Falastinu suka rusa dubban gidajen musulmi domin su kafa Isra’ila, a lokacin da Sudais yake kira zuwa ga kulla alaka da wadannan yahudawa, amma kuma ba a  taba jin ya yi tir da abin da suke aikatawa kan musulmin falastinu ba.

3921230

 

captcha