IQNA

An Fara Ginin Babbar Cibiyar Musulmi A Jihar Michigan A Amurka

22:26 - August 22, 2020
Lambar Labari: 3485111
Tehran (IQNA) an fara gudanar da ginin bababr cibiyar musulmi da ke hade da babban masallaci a jihar Michigan ta kasar Amurka.

Shafin yada labarai na Candg News ya bayar da rahoton cewa, a garin (Sterling Heights) daga cikin jihar Michigan a kasar Amurka musulmi sun fara ginin babbar cibiya ta (American Islamic Community Center)

Sam Sobh daya daga cikin mambobin kwamitin cibiyar ya bayyana cewa, wannan cibiya za ta kunshi bangarori daban-daban, da suka hada da masallaci da kuma wuraren karatu da taruka, gami da wuraren motsa jiki, inda har wadanda ba musulmi za su iya yin amfani da wurin matukar dai za su kiyaye sharuddan da za a gindaya.

Tun a cikins hekara ta 2016 ya kamata a fara ikin, amma wasu  masu adawa da musulmi suka nuna rashina mincewarsu, bisa hujjar cewa za  ajawo cunkoson ababen hawa a wurin, amma daga karshe an bayar da iznin gina cibiyar a hukumance.

Sobh ya ce sun yafe wa dukkanin wadanda suka kawo tsaiko ga shirin, kuma suna fatan wurin ya zama wata cibiya wadda za ta rika hada mabiya addinai daban-daban domin kara samun fahimtar juna da zaman lafiya da kuma karfafa ‘yan adamtaka.

 

3918077

 

captcha