IQNA

Martanin Musulmin Amurka Ga Trump Kan Izgilin Da Ya Yi A Kan Ibadar Watan Ramadan

23:07 - April 20, 2020
Lambar Labari: 3484727
Tehran (IQNA) Musulmin kasar Amurka sun mayar da martani mai zafi dangane da kalaman izgili da Trump ya yi a kan musulmi da kuma ayyukan ibada da suke gudanarwa a cikin watan Ramadan.

Shafin yanar gizo na babbar cibiyar musulmin kasar Amurka ta bayar da bayanin cewa, musulmin kasar suna yin tir da Allawadai da kalaman izgili da nuna wariya ga musulmin kasar da Trump ya yi, tare da bayyana cewa hakan ba zai raunana zukatan musulmin kasar wajen aiwatar da abin da ya dace da su ba.

A jiya ne, Donald Trump ya bayyan acewa, yana fatan ganin an dauki a kan musulmi wajen hana su gudanar da tarukansu na ibada a cikin watan Ramadan, kamar yadda aka dauki irin wannan matakin wajen hana mabiya addinin kirista gudanar da tarukansu a lokacin Easter, domin a cewarsa a Amurka ana nuna bambanci tsakanin mabiya addinin kirista da musulmi, inda ake barin musulmi su yi abin da suka ga dama, sabanin mabiya addinin kirista.

Shugaban bababr cibiyar musulmin kasar Amurka nahad Awwad ya bayyana cewa, musulmin Amurka sun riga Trump fahimtar hadarin da ke tattare da cutar corona, a kan haka tun kafin ya fahimci wannan hadarin, kwamitin malaman musumi a Amurka ya fitar da fatawar dakatar da tarukan da ake yi a cikin watan Ramadan, domin hana yaduwar wanann cuta a tsakanin jama’a.

Awwad ya ce furucin na Trump abin ban takaici ne, domin kuwa kalami ne na nuna wariya da bangaranci a tsakanin al’ummar kasar Amurka bisa banbancin addini ko akida, wanda hakan ya sabawa dokokin da suke rubuce a cikin kundin tsarin muslmin kasar.

3892872

 

captcha