IQNA

Za A Gudanar Da Taron Maulidin Imam Baqir (AS) A Vienna

23:48 - March 07, 2019
Lambar Labari: 3483432
Bangaren kasa da kasa a gobe ne idan Allah ya kai mu za a gudanar da taron maulidin Imam Muhammad Baqir (AS) a birnin Vienna na Austria.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, cibiyar Imam Ali (AS) da ke birnin Vienna na kasar Ausria tana da shirin gudanar da taron maulidin Imam Baqir (AS) a gobe idan Allah ya kai mu.

Muhammad Ali Muhsen zadeh na daga cikin malaman da za su gabatar da jawabi a wurin taron, kamar yadda kuma wasu daga cikin masu wakokin bege ga manzon Allah (SAW) da alayensu za su gabatar da nasu kasidu.

Cibiyar dai tana daga cikin manyan cibiyoyin mulsunci a kasar ta Austria, inda take gudanar da shirye-shirye da suka shafi addini tare da hada dukkanin musulmi daga koewane bangare na sunna da shi’a da sauransu, bayan samun lasisi a 2001.

A gobe ne daya ga Rajab ranar haihuwar Imam Baqir (AS).

3796044

 

 

 

 

 

 

captcha