IQNA

Fatah Ta Kirayi Taron Gaggawa Kan Batun Yarjejeniyar Karni

23:56 - July 05, 2018
Lambar Labari: 3482810
Bangaren kasa da kasa, Kungiyar Fatah karkashin jagorancin shugaban Falastinawa Mahmud Abbas, ta kirayi wani taron gaggawa domin tattauna batun yarjejeniyar karni kan Palestine.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a zaman da manyan kusoshin kungiyar Fatah suka gudanar, sun tattauna batun abin da ake kira yarjejeniyar karni kan Palestine, inda suka kira hakan a matsayin wata sabuwar yaudara domin kara tabbatar da kafuwar Isra'ial da kuma kwace hakkokin al'ummar Palestine.

Dukkanin mambobin Fatan sun amince a kan cewa ba za su taba amincewa da wannan shiri da suka kira na yaudara ba, wanda Amurka da Saudiyya da kuma Isra'ila suka shirya domin tabbatar da halascin Isra'ila, da kuma mamayar da take yi wa yankunan Falastinawa.

Bayanin taro ya tabbatar da cewa mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Quds mai alfarma daya ne daga cikin wannan shiri, haka nan kuma rusa yankunan Falastinawa da Isra'ila ta fara yia  cikin wannan mako a kudu maso gabashin birnin Quds, duk yana daga cikin wannan yaudara.

Amurka da Saudiyya gami da Isra'ila ne suka shirya wannan yarjejeniya a tsakaninsu da sunan warware rikicin Isra'ila da Falastinawa, amma yarjejeniyar ba ta kunshi kafa kasar Falastinu mai cin gishin kanta da bababn birninta na Quds ba, haka nan kuma dukkanin abubuwa da yarjejeniyar ta kunsa, abubuwa ne da za su kara tabbatar da kafuwar Isra'ila tare da kara danne al'ummar Falastinu tare da kuma kwace musu hakkokinsu.

3727752

 

 

captcha