IQNA

An Kawo Karshen Gasar Hardar Kur’ani Mai Tsarki Ta Duniya A Birnin Dubai

22:54 - July 05, 2015
Lambar Labari: 3323720
Bangaren kasa da kasa, an kawo karshen gasar karatu da hardar kur’ani mai ta duniya a birnin Dubai tare da halartar mahardata 76 daga kasashen duniya.


Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ktimes cewa, a jiya ne aka kammala gasar karatu da hardar kur’ani mai ta duniya a birnin Dubai tare da halartar mahardata saba’in da shida daga kasashen duniya, wadda aka gudanr har tsawon kwanaki 11 a jere ana karawa tsakanin makaranta 76 daga karshe kuma aka fitar da wadanda suka fi nuna kwazo.

Bayanin ya ci gaba da cewa dukkanin wadanda suka halarci gasar mutane 83 5 daga cikinsu alkalai ne, 7 kuma wadanda suka halarta ne, daga kasashen Ukraine, Trkiya, Senegal, Filland, Bosnia, maqadoni da kuma Belgium, wadanda suka bayar da gagarumar gudunmawa a wannan gasa.

Muhammad Abdulrahim Sultan ya ce ko shakka bau wannan gasa ta samu baabr nasara, domin kuwa babbar manufar it ace raya sakon addinin muslunci, tare da isar da shi hatta ga wadanda bas u da masaniya  akansa, kamar yadda kuma daya daga cikin manufofin it ace kara karfafa gwiwar musulmi kan kur’ani.

Ya ce sun aike da goron gayyata zuwa ga cibiyoyi kimanin 150 a kasashe daban-daban domin su aiko da masu karatu, kuma da dama daga cikinsu sun samu halarta, inda suka nuna kwazo matuka a cikin wannan gasa, wanda kuma hakan bababn abin fahari ne.

Sultan ya ci gaba da cewa idan aka yi la’akari da cewa tun kimanin shekaru 18 da aka fara gudanar da wannan shari na gasar kur’ani a Dubai za a fahimci irin gagarumin ci gaban da aka samu idan aka kwatanta da shekarun da suka gabata.

3323266

Abubuwan Da Ya Shafa: dubai
captcha