IQNA

Mahardata 34 Ne Suka Kai ga Matakin Karshe A Gasar Kur’ani Ta Duniya A Dubai

23:52 - June 29, 2015
Lambar Labari: 3321184
Bangaren kasa da kasa, mahardata 34 ne suka kai ga mataki na karshe a gasar karatu da hardar kur’ani ma tsarki ta duniya da k eke gudana ahalin yanzu a birnin Dubai.


Kafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na GToday cewa, bakwai daga cikin mahardatan sun fito ne daga kasashen Mauritani, Palastinu, Afirka ta kudu, Bahrain, Sirilanka, Muzambik da kuma Togo.

7 daga cikin wadanda za su kara da su kuma su ne Muhammad Zakariya daga kasar Bangaladash, Mujahid daga Yemen, Azam Iqbal daga Birtaniya, Abdullatif Yakub daga Ghana, Hasan Sammuh daga Thailand, Tan Su Maynamar, Abbasi Ahmad Ali Tanzania.

Muhammad Hussain Behzadfar daga jamhuriyar muslunci ta Iran na daga cikin masu halartar gasar da suka kai ga mataki na karshe a cikin gasar, inda yake halartar gasa ta biyu a wajen kasar bayan wadda a aka yi a shekarar da ta gabata.

An gabatar da laccoci har sau 22 a wurin wannan gasa, inda akan gayyaci malami daga sassa daban-daban na kasashen musulmi suna gabatr da jawabi tare da fatdakarwa kan muhimamn lamurran da suka shafi musulmi da kuma fadakarwa ta kur’ani mai tsarki.

A wurin wannan gasa ana gudanar da baje koli na kayyaki da suka shafi addinin muslunci da kuma al’adusa, domin nuna su ga mahalrta da kuma baki yan kasashen ketare da suke zuwa kasar da ake gayata suna dubawa.

Bayanin ya ce hakan yana da babban tasiri ga masu halarta musamman ma yan kasashen waje wadanda ba musulmi ba, inda suke nuna farin cikinsu matuka kan abubuwan da suke gani na burgewa dangane da addinin muslunci, har ma wasunsu kan musulunta.

3320761

Abubuwan Da Ya Shafa: dubai
captcha