IQNA - Taron "Maganin Jihohi Biyu" wanda kasashen Faransa da Saudiyya suka dauki nauyin shiryawa tare da halartar dimbin shugabannin kasashen duniya, an yi shi ne a birnin New York na kasar Amurka domin amincewa da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, inda aka jaddada cewa: Idan ba a samar da kasashe biyu ba, ba za a samu zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya ba; kafa kasar Falasdinu ba lada ba ne, amma hakki ne.
15:51 , 2025 Sep 23