IQNA

An Yi Alawadai Da Wani Fim Na Batunci Ga Harka Islamiyya A Najeriya

22:19 - September 14, 2020
Lambar Labari: 3485186
Tehran (IQNA) magoya bayan Harka Islamiyya a Najeriya sun yi Allawadai da kakkausar murya kan wani fim na yin batunci da cin zarafinsu da masana'antar fina-finai ta Nollywood take shiryawa.

Shafin yada labarai na The Will Najriya ya bayar da rahoton cewa, magoya bayan bayan Harka Islamiyya a Najeriya sun yi tir da Allawadai da wannan fim mai suna Fatal Arrogance, wanda a cikinsa ake kokarin bata fuskar harka Islamiyya, tare da nuna ta  a matsayin wani gungu na 'yan ta'adda.

Wani fitaccen dan fina-finan Nollywood mai suna Pete Edochie ne ya fito a matsayin babban tauraroa  acikin fim din inda yake a matsayin jagoran harka Islmiyya a cikin fim din.

Shugaban dandalin yada labarai na harka Islamiyya Ibrahim Musa ya fitar da wani bayani, wanda  a cikinsa ya bayyana wannan fim din a matsayin cin zarafi, wanda zai iya haifar da babbar matsala a kasar, a kan haka ya bukaci Nollywood da su sake yin nazari kan fim din tun kafin su fito da shi.

3922618

 

Abubuwan Da Ya Shafa: sheikh zakzaky babbar matsala
captcha