Kungiyar ‘yan jarida ta duniya ta fitar da bayanin yin Allawadai da kakkausar murya kan kisan Shireen, tare da dora alhakin hakan a kan gwamnatin Isra’ila, kamar yadda kungiyar ta bukaci da a gudanar da bincike kan lamarin, wanda zai kunshi bangarori na kasa da kasa.
Su ma a nasu bangaren Amurka da Tarayyar Turai da kuma Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Hadin Kan Kasashen Larabawa, da kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, duk sun bukaci da a gudanar da bincike na bangarori masu kansu kan wannan lamari.
A nata bangaren gwamnatin Falastinawa ta bayyana cewa, yanzu haka ta fara hada fayil-fayil kan wannan batu domin mika shi ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, domin shigar da kara a kan Isra’ila, dangane da kisan Shireen Abu Akleh.
Kungiyoyin Hamas, Hizbullah, Jihad Islami, Ansarullah ta Yemen (Alhuthi) da kungiyoyin gwagwarmaya a Iraki, duk sun fitar da bayanai na yin Allawadai da kisan Shireen.
Sojojin yahudawan Isra’ila sun harbe Shireen Abu Akleh ne a safiyar jiya a lokacin da take daukar rahoto a wani samame da sojojin Isra’ila suka kai kan Falastinawa a yankin Jinin da ke gabar yammacin Kogin Jordan a Falastinu.