IQNA

Falastinawa Suna Ci Gaba Da Mayar Da Martani Da Makamai Masu Linzami A Kan Hare-Haren Isra'ila

23:44 - May 12, 2021
Lambar Labari: 3485908
Tehran (IQNA) Falastinawa ‘yan gwagwarmaya sun mayar da martani da makamai masu linzami a kan muhimman biranan Isra’ila.

A cikin rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar,  kungiyoyin gwagwarmayar Falastinawa da ke yankin zirin Gaza, sun mayar da martani da makamai masu linzami a kan biranan Tel Aviv, Asqalan da kuma wasu matsugunnan yahudawan yahudawa ‘yan share wuri zauna.

Wannan martani dai yana zuwa ne bayan munanan hare-haren da Isra’ila ta kaddamar a kan yankin zirin Gaza, wanda ya yi sanadiyyar yin shahadar Falastinawa akalla 65, tare da jikkatar wasu fiye da 300, daga cikin wadanda suka shahada har da kananan yara 15 da mata biyar.

Tashar talabijin ta 13 ta gwamnatin yahudawan sahyuniya ta bayar da rahoton cewa, makaman da Hamas ta harba sun sauka a babban filin sauka da tashin jiragen sama na Ben Gurion da ke TelAviv, filin jirgi mafi girma na Isra’ila.

Baya ga haka kuma rahoton tashar yahudawan ya ce, Hamas ta ragargaza wasu manyan tankuna ajiyar makamashi na Isra’ila da ke yankin Asqalan, wadanda har zuwa tsakar daren jiya ‘yan kwana-kwanan Isra’ila ba su iya kashe wutar da ke ci a wurin ba.

Sannan kuma rahoton ya tabbatar da halakar akalla yahudawan sahyuniya uku da jikkatar wasu da dama sakamakon hare-haren martani na Falastinawa a kan yankunan da yahudawa suka mamaye.

Tun kimanin wata guda da ya gabata ne dai yahudawan sahyuniya masu tsatsauran ra’ayi suka fara tsokanar musulmi a masallacin Quds a daidai lokacin da aka shiga watan Ramadan mai alfarma, inda jami’an tsaron yahudawan Isra’ila suke ba su kariya, yayyin da su kuma Falastinawa suka dauki matakin hana yahudawan kutsa kai a cikin masallacin mai alfarma, wanda daga hakan ne rikicin ya ci gaba har zuwa wannan lokaci

 

3971025

 

 

captcha