IQNA

Kungiyar Kasashen Larabawa Za Ta Gudanar da Zaman Gaggawa Kan Batun Quds

23:45 - May 09, 2021
Lambar Labari: 3485897
Tehran (IQNA) Kungiyar kasashen larabawa za ta gudanar da zaman gaggawa dangane da farmakin da yahudawan sahyuniya na Isra’ila suke kaddamarwa a kan Falastinawa mazauna birnin Quds.

Shafin yada labarai na jaridar Akhbar Yaum ya bayar da rahoton cewa, a cikin bayanin da ta fitar, kungiyar kasashen larabawa ta sanar da cewa, ranar Talata za ta gudanar da zaman gaggawa dangane da farmakin da yahudawan sahyuniya na Isra’ila suke kaddamarwa a kan Falastinawa mazauna birnin Quds, wanda ministocin harkokin wajen kasashen mamba a kungiyar za su halarta.

Ita ma a nata bangaren kungiyar tarayyar turai ta nuna takaicinta matuka dangane da abin da yake faruwa, tare da kiran dukkanin bangarori na Isra’ila da kuma Falastinawa da su kai zuciya nesa, tare da nisantar keta alfarmar wurare masu tsarki na ibada da suke birnin Quds.

Tun kafin wannan lokacin dai kungiyar tarayyar turai ta nuna rashin amincewarta da matakan da Isra’ila take dauka na mamaye yankunan Falastinawa a gabashin birnin Quds, da kuama wasu yankuna da ke gabar yammacin kogin Jordan, inda tarayyar turai ta bayyana hakan a matsayin aikin daya sabawa dokokin kasa da kasa.

 

3970171

 

captcha