IQNA

Ana Ci Gaba Da Yin Tir Da Isra’ila Kan Farmakin Da Take Kaiwa Falastinawa A Birnin Quds

23:48 - May 08, 2021
Lambar Labari: 3485891
Tehran (IQNA) ana ci gaba da yin tir da farmakin da jami’an tsaron Isra’ila suka kaddamar kan masallacin Quds.

Kasashen musulmi da dama sun yi tir da farmakin da jami’an tsaron Isra’ila suka kaddamar kan masallacin Quds, lamarin da ya yi sanadin jikkatar falasdinawa sama da dari biyu.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Sa’eed Khatibzadeh ya ce Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta “yi Allah wadai” da mamayar da Isra’ila ta yi wa Masallacin al-Aqsa, Kiblar farko ta Musulmai.

Ya kara da cewa "Wannan laifin na yaki ya sake nuna wa duniya halin aikata laifi na yahudawan sahyuniya da kuma bukatar daukar matakin gaggawa na kasa da kasa don dakatar da take hakkokin dan adam da na dokokin kasa da kasa," in ji shi.

Ita ma ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya a cikin wata sanarwa ta ce "tana matukar yin Allah wadai" da harin na ranar Juma'a da sojojin Isra'ila suka kai kan Falasdinawa masu ibada a Masallacin al-Aqsa.

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya fada a shafinsa na Twitter inda ya ce, "Rashin mutuntaka ne Isra'ila ta far wa marassa laifi da ke Sallah a lokacin Azumin Ramadan."

Haka ma kasashen Qatar, Kuwait, Masar duk sun la’anci farmakin na Isra’ila a masallacin na Quds.

Ita ma Jami'ar al-Azhar ta Masar, ta danganta lamarin da abin kunyar kan yadda kasashen duniya suka kasa tsawata wa Isra’ial game da abin da ke faruwa a al-Quds.

Saudiyya dai bata yi allawadai da lamarin ba, amma ta ce abunda Isra’ila ke yi na ruguza duk wani yunkuri na samar da zaman lafiya.

A wani labarin kungiyar tarayyar turai, ta bukaci Isra’ila ta duk abunda ya dace domin kwantar da hankali.

 

3969936

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: kasashen duniya zaman lafiya
captcha