IQNA

Miliyoyin Mutane Ne Suka Ziyarci Baje Kolin Kur'ani Ta Hanyar Yanar Gizo A rana Ta Farko

22:55 - May 02, 2021
Lambar Labari: 3485868
Tehran (IQNA) miliyoyin mutane suka ziyarci baje kolin kur'ani kur'ani mai tsarki ta hanyar yanar gizo a ranar farko.

Bisa rahoton da kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar, miliyoyin mutane suka ziyarci baje kolin kur'ani kur'ani mai tsarki ta hanyar yanar gizo a ranar farko da fara wannan baje koli.

An fara gudanar da baje kolin ne dai a jiya ta hanyar yanar gizo, inda fiye da mutane dubu 95 suka wata shafin baje kolin zuwa wasu shafuka daban-daban ta hanyar yanar gizo, wanda hakan yasa miliyoyin mutane suka ziyarci shafin cikin sauki.

A wannan baje kolin dai ana nuna muhimman abubuwa da suka shafi kur'ani mai tsarki, daga ciki har da hotuna na dadaddun kwafin kur'anai.

Baya ga haka kuma akwai alluna da aka rubuta da salon fasahar rubutu na larabci wanda aka rubuta ayoyin kur'ani da salo mai kyau mai daukar hankali da abn sha'awa.

Sannan kuma akwai wasu daga cikin zane-zane da aka yi wadanda suke ishara da wasu abubuwa ad suka zo cikin kur'ani, kamar kisoshin annabawa ko labarin wasu birane, ko ayoyi da suke bayani kan hikimomin da ke tatatre da halittar sammai da kassai da sauran ayoyi na ubangiji da ke tabbatar da samuwar Allah madaukakin sarki da ikonsa a kan dukkanin talikai.

 

 

 

3968683

 

captcha