A zantawarsa da kamfanin dillancin labaran Iqna Ayatollah Sayyid Muhammad Gharawi ya bayyana cewa, daren Lailatul Qadr wata babbar dama ce ta tuba zuwa ga Allah daga zunubbanmu, wadda bai kamata mu yi saku-saku da ita ba.
Ya ci gaba da cewa, baya da falala da take a cikin watan ramadan, akwai falala ta musamman a cikin dararen Lailatul Qadr wadda ta ninka sauran falaloli da sauran ranaku da dararen da suke cikin wannan wata mai alfarama.
Malamin ya kara da cewa, ba ya ga ayyuka na nafila da mustahabbi, hatta ayyuka na wajibi Allah madaukakin sarki yana ninka ladarsu sau saba'in idan aka yi yi a cikin daren lailatul Qadr, da hakan ya hada da salloli na wajibi da zakka da sauransu.