IQNA

An Nuna Wasu Dadaddun Kwafi-Kwafin Kur'ani Da Aka Rubuta Daruruwan Shekaru A Sharjah UAE

23:46 - April 30, 2021
Lambar Labari: 3485862
Tehran (IQNA) an nuna wasu dadaddun kwafi-kwafin kur'ani mai tsarki da aka rubuta daruruwan shekaru da suka gabata a wani baje koli a garin Sharjah na kasar UAE.

Shafin yada labarai na Emarate Yaum ya bayar da rahoton cewa, an nuna wasu dadaddun kwafi-kwafin kur'ani mai tsarki da aka rubuta daruruwan shekaru da suka gabata a wani baje koli a garin Sharjah na kasar hadaddiyar daular larabawa.

A wannan baje baje koli ana nuna tsoffin kwafin kur'anai da aka rubuta a lokuta daban-daban a karnononin da suka gabata.

Daga ciki akwai wadanda an rubuta sua  lokacin daular Usamaniya, wasu kuma an rubuta su ne tun kafin lokacin daular Usmaniya, wanda hakan ke nuna cewa an rubuta kur;anan ne daruruwan shekaru da suka gabata.

Hukumar ad ke kula da adana kayan tarihi a birnin Sharjah na kasar hadaddiyar daular larabawa wato UAE, tana kashe makudan kudade wajen tattarawa da kuma samo irin wadannan kwafin kur'anai a kasashen larabawa daban-daban.

نمایش صدها نسخه خطی نادر قرآن در شارجه

 

3968122

 

captcha