IQNA

Yahudawan Isra'ila Sun Sake Auka Wa Musulmi A Lokacin Sallar Asham A Masallacin Quds

23:57 - April 25, 2021
2
Lambar Labari: 3485846
Tehran (IQNA) Jami’an tsaron gwamnatin yahudawan Isra’ila sun sake auka wa masallata a daren jiya a lokacin sallar Isha’i da asham.

A rahoton da kamfanin dillancin labaran Iqna ya bayar, daruruwan jami’an tsaron Isra’ila ne dauke da bindigogi da kuma motoci masu sulke suka killace masallacin Aqsa a lokacin da musulmi suke gudanar da sallar Isha’i da kuma sham a daren jiya.

Bayan kammala sallar, jami’an tsaron an Isra’ila sun fara harba hayaki mai sanya hawaye a kan masallatan, kamar yadda kuma suka shiga dukarsu da kulake a lokacin da suke fitowa daga cikin masallacin mai alfarma.

حمله نظامیان صهیونیست به نمازگزاران فلسطینی در مسجدالاقصی

Jami’an tsaron gwamnatin yahudawan sun jikkata wasu daga cikin musulmi Falastinawa da suka yi salla a daren jiya a masallacin Aqsa, yayin da kuma suka kame suka yi awon gaban da su, wadanda ba a san makomarsu ba.

حمله نظامیان صهیونیست به نمازگزاران فلسطینی در مسجدالاقصی

Ko a daren Alahamis da ta gabata ma yahudawa masu tsatsauran ra’ayi sun kai farmaki kan masallata a cikin masallacin na Quds, tare da lakada wa wasu daga cikin musulmi da suka yi salla a wurin duka.

حمله نظامیان صهیونیست به نمازگزاران فلسطینی در مسجدالاقصی

A ranar Juma’ar da ta gabata ma sun dauki matakan hana musulmi sun yi sallar Juma’a a cikin masallacin, amma duk da haka kimanin musulmi dubu saba’in da biyar ne suka yi sallar Juma’a a cikin masallacin Quds.

3966909

 

 

Wanda Aka Watsa: 2
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Hassan Muhammadu
0
0
Wannan zalumcine amma allah yasaka musu amma allah yakaramusu jurira da imani
Amsoshi
sulaiman ahmad
ya allah albarkaci wana wata kasa kawa falasdinawa
captcha