IQNA

Jakadan Kasar Ghana A Iran Sanye Da Tufafin Kente A Yayin Ganawa Da Rauhani

23:49 - March 03, 2021
Lambar Labari: 3485708
Tehran (IQNA) sabon jakadan kasar Ghana a kasar Iran ya mika takardunsa na fara aiki, amma kuma sanye tufafin Kente na al’adar kasar  Ghana lamarin da ya burge jama’a da dama.

Muhammad Mohsen Maarifi masani kan harkokin tarihi kuma mamba a kwamitin masu bincike na ilimi a jami’ar Almustafa, ya bayyana matsayin wannan al’ada ta saka irin wannan tufafi a kasar Ghana da cewa yana da asali na daruruwan shekaru a baya.

Ya ce saka wannan tufafi yana dauke da ma’anoni da dama, daga ciki har da nuna tsohuwar al’ada da suka gada iyaye da kakanni.

Baya ga haka kuma ita ce shiga ta dattijai, wanda duk wanda ya saka tufafi irin haka to tabbas dattijo ne da yake da girma a wurin jama’arsa.

Sannan kuma ya kara da cewa, daya daga cikin abubuwa da al’ummomin Afirka suka kebanta da su, shi ne riko da kuma kiyaye al’adunsu da suka gada iyaye da kakanni, wanda daya daga cikin misalin hakan shi ne saka wannan nau’in tufafi da mutanen kasar Ghana suke yi.

Baya ga mutanen kasar Ghana, al’ummomi da dama a yankuna daban-daban musamman a yammacin nahiyar Afirka, an san su da girma al’adunsu da kuma kiyaye su.

Baya ga cewa tufafin Kente na mutanen Ghana tufafi   ne da ake samarwa daga yadi na musamman mai nagarta, a lokaci guda kuma yana dauke da kaloli daban-daban masu sanya nishadi da farin ciki.

3957300

 

captcha