IQNA

China Tana Takura Wa Musulmin Uyghur Da Sunan Yaki Da Tsatsauran Ra’ayi

19:06 - February 21, 2021
Lambar Labari: 3485675
Tehran (IQNA) a cikin shekarun baya-bayan nan gwamnatin kasar China tana daukar matakai na takura wa musulmin Uyghur na kasar da suna yaki da tsatsauran ra’ayi.

A wata zantawa da ya yi da kamlfanin dillancin labaran iqna, Isa Dulkun shugaban gayammar kungiyoyin musulmin kabilar Uyghur na duniya, kuma dan siyasa mai wakiltar yankinsa a kasar China, ya bayyana cewa, ko shakka babu a cikin shekarun baya-bayan nan gwamnatin kasar tana daukar matakai na takura wa musulmin Uyghur na kasar da suna yaki da tsatsauran ra’ayi, wanda hakan ba gaskiya ba ne.

Isa Dulkun wanda aka Haifa a ranar 2 ga watan Satumban shekara 1967 a yankin Xinjiang, wanda mafi mazaunan yankin msuulmi ne ‘yan kabilar Uyghur, wanda shi ma daya ne daga cikin ‘ya’yan wannan kabila.

اقدامات دولت چین علیه اویغورها جنگ علیه اسلام است

Ya ce daukar matakan nuna musu wariya da mahukuntan China suke yi ba sabon lamari ba ne, amma dai a cikin shekarun baya-bayan nan lamarin yafi tsananta, sakamakon daukar matakai da ake na hana su gudanar da harkokinsu na addini, bisa wasu hujjoji marasa tushe.

Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, ana kiransu da kabila marasa rinjaye a kasar China, ya ce sub a marasa rinjaye ba ne, domin kuwa su ‘yan kasar China ne kamar kowa, suna hakki kamar kowane mutuma  kasar amatsayinsa na dan kasa, to amma dukkanin matsalolin ad suke fuskanta da banbancin da ake nuna musu saboda su musulmi ne kawai, ba domin su ba ‘yan kasar China ba ne.

Daga karshe ya yi kira da cewa, su babban abin da suke bukata shi ne adalci, a daina zalu8ntarsu, a bar su su yi addininsu ba tare da tsangwama ba, kamar yadda kuma ya bayyana cewa, kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya sun yi kokari matuka wajen bayana wa duniya irin mawuyacin halin da musulmi ‘yan kabilar Uyghur suke ciki a kasar China.

3955066

 

captcha