IQNA

Shekhul Azhar: Dole Ne A Karfafa Tattaunawa Tsakanin Musulmi Da Kiristoci

23:03 - October 11, 2019
Lambar Labari: 3484143
Bangaren kasa da kasa, babban malamin Azhar ya yi kira zuwa karfafa tattaunawa tsakanin mabiya addinan musulunci da kiristanci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin yada labarai Sadal Balad cewa, a wata tattaunawa da ta gudana tsakanin Ahmad Tayyib babban malamin Azhar da kuma jakadan Birtaniya a Masar Jefry Adams a jiya, malamin ya jaddada wajabcin fadada tattaunawa tsakanin mabiya addinan musulunci da kiristanci a duniya.

Ahmad Tayyib ya bayyana cewa, kara samun fahimtar juna tsakanin mabiya addinain musulunci da kiristanci a  duniya, yana da gagarumin tasiri wajen ci gaban duniya da ma zaman lafiya.

Ya ce a kwanakin bayan sun tattauna wannan batu tare da paparoma, kuma sun cimma matsaya kan yin dukkanin kokari tsakanin fadar Vatican da kuma cibiyar Azahar domin kaiwa ga wannan manufa, kuma bangarorin biyu suna ci gaba da tuntubar juna.

Shi ma a nasa bangaren jakadan na Birtaniya a Masar ya bayyana gamsuwar kasarsa da wannan mataki.

3848967

 

 

 

captcha