IQNA

Qasemi: Iran Na Allawadai Da Kisan Gillar Saudiyya A Kan Fararen Hular Yemen

21:42 - March 11, 2019
Lambar Labari: 3483444
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya bayyana harin da Saudiyya ta kai a jiya kan fararen hula tare da yi musu kisan gilla a gundumar Hajjah ta kasar yemen da cewa abin takaici ne.

Kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da tarin manema labarai yau a birnin Tehran Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya ce, ina kasashe masu karyar kare hakkokin bil adama, mene dalilin da yasa ba a ji duriyarsu ba bayan kai harin da Saudiyya ta yi jiya  akan dararen hula da yi musu kisan gilla?

Ya ce mai makon hakan ma su ne kan gaba wajen sayar da wadannan makaman da ake kai harin da su a kan fararen hula da masallatai da kasuwanni da cibiyoyin da gidajen jama'a, kuma tun da suna samun ribar sayar da makamansu a wurinsu yin haka ba laifi ba ne.

Qasemi ya ci gaba da cewa, yana kira ga masu aikata wannan mummanan aiki na rashin imani da tausayi a kan mata da kananan yara da su ji tsoron Allah matukar sun yi imani da shi.

Tun a cikin watan Maris na 2015 ne Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare kan al'ummar kasar yemen bisa hujjar yaki da 'yan kungiar Alhuthi, inda ya zuwa bisa alkalumman kungiyoyin kasa da kasa, ta kashe dubban fararen hula da suika hada da mata da kanana yara a wadannan hare-hare.

3796896

 

captcha