Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayyana cewa a ci gaba da hare-haren da jiragen yakin HKI suke kaiwa kan yankin Gaza, a safiyar yau Asabar, mayakan rundunar Izzuddeen Qassam reshen soja na kungiyar Hamsa 4 ne suka yi shahada.
A daren jiya jumma dai dakarun izzuddeen Qassam biyu ne suka yi shahada. Har'ila yau ma'aikatar lafiya ta Palasdinawa ta bada sanarwan cewa daga ranar Alhamis zuwa jiya jumma'a Palasdinawa 1,114 ne suka ji raunuka daban daban.
A ranar Laraban da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donald Trump ya bada sanarwan amincewa da birnin Quds ya zama cibiyar mulkin HKI, wanda ya fusata al-ummar Palasdinu da kuma kasashen duniya da dama.
Yanzu haka dai wannan matai ya sanya dukkanin al'ummomin musulmi a koina cikin duna suna ta gudanar da jerin gwanon rashin amincewa, tare da yin Allah wadai, da kuma kiran a dauki matakin kaurace ma yahudawa da Amurka a kasashen musulmi.